Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya taya takwararsa ta kasar Singapore murnar cika shekaru 55 da kafuwar kasar
2020-08-09 16:28:30        cri

Yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga wa takwararsa ta jamhuriyyar Singaore Halimah Yacob wayar tarho domin taya ta murnar cika shekaru 55 da kafuwar kasarta.

A cikin hirarsu, Xi ya nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 55 da suka gabata, Singapore ta bullo da wata hanya da ta dace don samun bunkasuwar kasar, Sin tana jinjinawa sabbin ci gaba da kasar take samu. A cewarsa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana samun bunkasuwa yadda ya kamata, kuma suna hadin kansu a fannoni daban-daban, matakin da ya zama abin koyi ga sauran kasashe. Sin tana dora babban muhimmanci kan bunkasuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu, tana mai fatan kara hadin kan kasashen biyu bisa zarafi mai kyau na cika shekaru 30 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakaninsu a bana, don ingiza dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabo matsayi. (Amina)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China