Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Motsa jiki yana da amfani matuka, ba bata lokaci ba ne
2020-08-08 17:11:20        cri

A ranar 8 ga watan Agustan shekarar 2008, aka kaddamar da taron wasannin Olympic a nan birnin Beijing, kuma tun daga shekarar 2009, kasar Sin ta kebe ranar 8 ga watan Agusta a matsayin ranar motsa jiki ta al'mmun Sinawa. Babban taken ranar a bana shi ne "Ingiza motsa jikin daukacin al'ummun Sinawa domin taimakawa tabbatar da matsakaicin wadata".

Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ba ilimi kadai mutum ke bukata ba, inda ya ce ya kamata ya kasance mai hali na gari da jiki mai karfi, don haka ya dace a kara kyautata ingancin lafiyar daukacin al'ummun Sinawa ta hanyar motsa jiki.

A ranar 7 ga watan Fabrairun shekarar 2014, shugaba Xi ya zanta da manema labaran gidan talibijin na kasar Rasha dake birnin Sochi, inda ya bayyana cewa, motsa jiki ba bata lokaci ba ne, domin yana da amfani matuka.

Yayin da yake rangadin aiki a lardin Shandong na kasar ta Sin a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2018, shugaba Xi ya bukaci a kara kebe filayen motsa jiki ga jama'a ta yadda al'ummun kasar za su kara jin dadin rayuwa.

Yadda al'ummun kasar suke motsa jiki da yadda kasar take gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashe a bangaren motsa jiki muhimman alamu ne dake nuna matsayin zamanintar da kasar. Kawo yanzu da aka cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ingancin lafiyar al'ummun kasar ya kyautata a bayyane, haka wasanni kan kankara sun dace da muradun shekaru dari daya guda biyu: wato "kafa zaman al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni a yayin da JKS ke cika shekaru 100 da kafuwa, da kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani mai wadata, bisa tsarin demokuradiya, wayin kai da kuma jituwa nan da shekara 2049, wato yayin bikin cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar Jama'ar Sin".

Za a shirya taron wasannin Olympic na lokacin hunturu a birnin Beijing a shekarar 2022, taron da zai sa kaimi kan al'ummun kasar domin kara nuna kuzari kan wasannin Olympic, haka kuma zai ingiza ci gaban wasannin kan kankara na kasar. A halin yanzu, al'ummun Sinawa da yawansu ya kai sama da miliyan 300 sun riga sun fara wasanni kan kankara a karkashin kiran shugaba Xi Jinping, lamarin da zai taka rawar gani kan ci gaban wasannin Olympic.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China