![]() |
|
2020-07-31 21:06:43 cri |
Shugaba Xi ya ce, marigayi Mkapa fitaccen shugaba ne a kasar Tanzaniya har ma a nahiyar Afirka, kuma aboki na kwarai ga kasar Sin, wanda ya bayar da babbar gudummawa ga yaukaka dangantakar dake tsakanin Sin da Tanzaniya da ma Afirka baki daya.
Xi ya ce yana maida hankali sosai ga raya huldar kasashen biyu, yana kuma fatan ci gaba da kokari tare da shugaba Magufuli, wajen ciyar da dangantakar abokantakarsu bisa manyan tsare-tsare gaba, da kara kawo alfanu ga daukacin jama'ar sassan biyu. (Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China