Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Trump Na Yunkurin Neman Moriya Daga Shawarwarin Tik Tok
2020-08-06 14:27:28        cri

Ya zuwa yanzu, ba a san makomar Tik Tok a Amurka ba. Amma, wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma ciki har da BBC, Reuters da dai sauransu, sun nuna rashin jin dadinsu game da matakin da gwamnatin Donald Trump ke dauka, wadda ta tilasta hana amfani da Tik Tok a Amurka, daga baya kuma ta canja ra'ayinta zuwa samun moriya daga hadewa da kamfanin Microsoft zai yi, a ganin wadannan kafofin, matakin da gwamnatin Amurka ke dauka tamkar kungiyar 'yan fashi ta Mafia, watakila za a kai kara kan wannan batun.

Charlotte Jee, dan jarida ta mujallar "MIT Technology Review" ta Amurka ya shedawa manema labarai na BBC cewa, maganar Donald Trump ta girgiza mutane sosai, matakin da ya dauka irin na kungiyar 'yan fashi, ba a taba ganin irinsa ba. A makon da ya gabata, masu kafa dokokin Amurka sun tattauna kan ko kamfanonin kimiyya suna gudanar da babakare ko a'a, amma matakin da Donald Trump ya dauka zai mai da wani kamfani ya yi girma kadai, abin mamaki ne.

Jiya Laraba, Reuters ta ba da labari cewa, Donald Trump ya tilasta kamfanin ByteDance na kasar Sin da ya biya Amurkar kudi idan ya sayar da Tik Tok, abin da ba a taba ganin irinsa ba, matakin da zai haddasa matsalar doka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China