Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mujallar New Yorker: jawabin Mike Pompeo dake sukar kasar Sin ya illata daddun muradun Amurka
2020-08-05 13:36:20        cri
Mujallar New Yorker, mai wallafa bayanai mako - mako a shafin intanet, ta wallafa wata mukala dangane da jawabin da sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya gabatar a dakin karatu na Richard Nixon a 'yan kwanakin baya, inda ta ce ya illata dadaddun muradun Amurka da kuma shelanta gazawar manufofin gwamnatinta a kan kasar Sin.

Mujallar ta ruwaito J Stapleton Roy, tsohon jakadan Amurka a Sin, a shekarun 1990 na cewa, sukar kasar Sin ba tare da tunani ba, rashin fahimta ce ta yanayin da ake ciki a kasar da yankin gabashin Asiya. Ya ce da yawa daga cikin kawayen Amurka na hulda da kasar Sin, kuma cinikayya a tsakaninsu na da yawa, kana kasashen gabashin Asiya ba sa son rikici. Ya ce kasar Sin tana ba al'ummarta damar rayuwa cikin wadata a wani mataki na sauri da ba a taba gani ba. Inda ya ce, yaudarar kai irin na Amurka, yunkurin diflomasiyya ne mai hadari.

Mujallar New Yorker ta yi tsokaci cewa, Mike Pompeo ya tabbatar da tattalin arzikin kasar Sin na da alaka mai zurfi da na Amurka da sauran kasashen duniya, amma duk da haka ya yi ikirarin Sin na dogaro da Amurka fiye da yadda Amurka ke dogaro da ita. Sai dai, hakikanin batu shi ne, yawancin abubuwan bukatun yau da kullum dake Amurka na kasar Sin ne, haka kuma kasar Sin ce ta biyu mafi samar da sassan motoci a Amurkar.

Har ila yau, mukalar ta ruwaito jawabin da Robert Zoelick, tsohon shugaban bankin duniya ya yi a watan Yuli, inda yake cewa, cikin shekaru 20 da suka gabata, kasar Sin ta bada gagarumar gudunmuwa ga ci gaban duniya, haka zalika a nan aka fi samun karuwar bukatar kayayyakin da Amurka ke fitarwa.

Bugu da kari, mukalar ta ruwaito, Kurt Campbell, tsohon mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka, ya yi hasashen cewa, kasar Sin za ta mamaye matakai mafi muhimmanci na manufofin Amurka a kasashen waje a zamani na gaba.

Sai dai, manufar Amurka kan Kasar Sin a yanzu, ya haifar da 'yar tsama da fito-na-fito tsakanin kasashen biyu, kuma wannan zai haifar da wasu abubuwan da ba za a iya hasashensu ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China