Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bakaken fatar Amurka 7 cikin duk mutum 10 sun san wanda 'yan sanda suka taba cin zarafi
2020-08-04 10:57:54        cri

Wasu alkaluman jin ra'ayin jama'a da cibiyar Gallup ta fitar, sun nuna cewa, kimanin kaso 71 bisa dari na bakaken fata Amurkawa, wato kimanin mutum 7 cikin duk mutum 10 sun san wani ko wasu da 'yan sanda suka taba cin zarafi, adadin da ya dara na sauran rukunin al'ummar Amurkawa, kana ya ninka na fararen fata har sau biyu.

Alkaluman sun kuma bayyana cewa, wannan adadi ya fi Kamari tsakanin matasa bakaken fata 'yan tsakanin shekaru 18 zuwa 44, wanda ya kai kaso 83 bisa dari na rukunin bakaken fatar kasar.

Kaza lika binciken ya shaida cewa, kaso 51 bisa dari na Amurkawa 'yan asalin Asiya sun san wadanda jami'an tsaro suka taba tursasawa, yayin da kaso 48 bisa dari na 'yan asalin Latin Amurka, da kaso 34 bisa dari na fararen fata dake kasar su ma sun ce suna da wannan masaniya.

A hannu guda kuma, rabin bakaken fatar kasar sun bayyana cewa, sun san wasu ko tarin wasu 'yan uwan su bakaken fata da aka daure a kurkuku ba bisa ka'ida ba, adadin da ba shi da yawa idan an kwatanta da na fararen fata, da 'yan asalin Asiya, da kuma tsakanin 'yan asalin Latin Amurka.

Binciken ya nuna cewa, tasirin matakan bincikar mutane ba bisa ka'ida ba, ko barazana, ko muzguna musu ko daure su, wanda ke da nasaba da ayyukan 'yan sanda, na da matukar illa da ta zarce batun daidaikun mutane, duba da cewa hakan na shafar yanayin hangen da al'ummu ke wa matsugunansu, da ma hukumomi ko gwamnatocin dake mulkar su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China