Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya ce ba shi niyyar jinkirta zaben shugaban kasa a watan Nuwanba
2020-07-31 13:57:44        cri
Shugaba Donald Trump na Amurka, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ba shi da niyyar jinkirta zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Nuwanba, bayan da a baya ya nemi a jinkirta zaben a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na tiwita.

Trump ya shaidawa taron manema labarai a fadar white House cewa, "ban ce a canja ranar zabe ba, kuma ban ce ina so a jinkirta zaben ba. Ina so a gudanar da zabe. Amma ba na son zabe da ba shi ne ba", inda ya soki tsarin zabe ta gidan waya.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na tiwiti jiya da safe, Trump ya yi ikirari ba tare da wata hujja ko shaida ba cewa, zaben shekarar 2020 ta hanyar gidan waya, ka iya zama mafi samun matsala da gardandami a tarihin zaben kasar.

Nan da nan dai, sakon da ya wallafa ya haifar da muhawarar siyasa tare da janyo suka daga majalisun dokokin kasar dake Capitol Hill, yayin da masana harkokin shari'a suka ce, Trump ba shi da ikon jinkirta zaben shugaban kasar, yayin da kundin tsarin mulkin kasar kuma ya baiwa majalisa ikon tsayar da ranar zaben.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China