Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka tana karancin kudin tallafawa marasa aikin yi
2020-08-03 10:54:31        cri

Majalisar dokokin Amurka, ta amince da ware dala triliyan 2 a karshen watan Maris da ya gabata, don tallafawa mutane da suka rasa ayyukan yi, kari kan kudin tallafi da yawansa ya kai dala 600 ga duk mutum a ko wane mako, wanda gwamnatocin jihohi daban-daban suka samarwa don tallafawa marasa aikin yi, bisa tushen kudin da aka tanadi tun da farko wanda ya kare a karshen watan Yuli. To sai dai kuma, ya zuwa ran 1 ga watan Agustan nan, jam'iyyar Dimokarat, da Republican ba su kai ga cimma matsaya daya kan karin kudin tallafin da za a samar a sabon zagaye ba.

Jaridar "The Wall Street" ta ba da labarin cewa, kudin tallafi ga duk mutum a ko wane mako ya ragu zuwa dala 200, cikin wani daftarin shiri da jam'iyyar Republican ta gabatar a kwanan baya, ta nuna cewa, matakin ya fuskanci rashin jin dadin 'yan jam'iyyar Dimokarat, bangaren da yake fatan a ci gaba da baiwa marasa aikin yi kudin tallafi da ya kai dala 600 a ko wane mako kafin watan Jarairu na shekarar badi.

Fadar shugaban kasar, da kuma jam'iyyar Republican, sun bayyana sau da dama cewa, dala 600 a kowane mako, za su rage kuzarin aiki na jama'a. Amma, a ganin Paul Krugman wanda ya taba lashe lambar Nobel a fannin tattalin arziki, ko da yake akwai irin wannan illa, amma ba za ta yi yawa ba, kuma kudin tallafin zai kara bunkasa bukatun cikin gida, ta yadda za a samar da karin guraben aikin yi ga Amurkawa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China