Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a gudanar da babban zaben Amurka a Nuwamba kamar yadda aka tsara
2020-08-03 14:00:01        cri

Shugaban ma'aikatan fadar White House ta Amurka Mark Meadows, ya ce za a gudanar da zaben shugaban kasar Amurka a ranar 3 ga watan Nuwambar dake tafe kamar yadda aka tsara.

Mark Meadows ya bayyana hakan a jiya Lahadi, yayin zantawa da kafar watsa labarai ta CBS, bayan da a baya shugaban Amurka Donald Trump ya yi wani tsokaci dake nuni ga yiwuwar dage zaben.

Kalaman Mr. Meadows sun karfafa matsayar mai baiwa shugaba Trump shawara a fannin yakin neman zabe Jason Miller, wanda shi ma kafar labarai ta Fox News ta raiwato shi yana cewa, za a kara kuri'u a babban zaben kasar ranar 3 ga watan Nuwambar bana, kuma a cewar sa wannan ne ra'ayin shugaba Trump.

A ranar Alhamis din makon jiya ne dai shugaba Trump, ya bayyana damuwarsa game da zaben dake tafe, yana mai nuni ga yiwuwar dage zaben, wanda ya ce yinsa a watan Nuwamba ta kafar gidan waya zai haifar da rudani. Kuma mai yiwuwa ya zamo zabe mafi rashin inganci a tarihin Amurka. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China