Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cha Guangju na jagorantar 'yan kananan kabilu mata wajen raya sana'o'i
2020-07-08 11:15:46        cri
A ranar 3 ga watan nan, Cha Guangju, 'yar kabilar Yi, kana mataimakiyar shugaban kungiyar hada kan kananan kabilu ta gundumar Xiangshan dake birnin Ningbo na lardin Zhejiang a nan kasar Sin, ta ziyarci babbar rumfar shuka inabi, a gabar da lokacin girbi inabin ke karatowa, inda take sa ran samun yabanya mai armashi.

Cikin shekaru 20 da suka gabata, fadin gonakin shuka inabi na Cha Guangju ya habaka, daga muraba'in mita dubu 2.7, zuwa muraba'in mita dubu 13.3. Kaza lika cikin wadannan shekaru 20, ta ba da taimako ga maigidan ta wajen biyan dukkan bashinsa, da gyara tsohon gidansu, har ma ta ba da jagoranci ga matan kauyen Xiaotang, wajen raya sana'o'i iri daban daban, domin neman samun wadata.

Cha Guangju ta ce, akwai matan kanannan kabilu sama da 50 da suka yi aure a kauyen Xiaotang, gabilin daga cikinsu, sun taba fama da talauci. Shi ya sa ta kan yi musayar ra'ayoyi da wadannan 'yan uwa na ta, domin neman wadata cikin hadin gwiwa.

Ya zuwa yanzu, bisa jagorancin Cha Guangju, ana samun karuwar 'yan kananan kabilu mata dake neman raya sana'o'i daban daban, domin samun karin kudaden shiga, da kyautata zaman rayuwarsu, bisa kokarin da suke yi. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China