Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump yana neman a jinkirta zaben shugaban kasar Amurka a watan Nuwanba
2020-07-31 09:50:37        cri

Shugaba Donald Trump na Amurka a jiya Alhamis, ya yi kira da a jinkirta zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwanba, yana mai zargin cewa, tsarin zabe ta gidan waya, zai iya haifar da mummunan magudi a zaben na shekarar 2020 a tarihin zabukan kasar. Kuma hakan a cewarsa, ka iya zama abin kunya ga Amurka.

A don haka, ya nemi da a jinkirta zaben har zuwa lokacin da mutane za su ji cewa, sun samu damar kada kuri'unsu cikin kariya da kuma sirri.

Shugaban ya wallafa sakon ne shafinsa na Tiwiti a wannan rana, lokacin da ma'aikatar kasuwanci kasar ta ba da rahoton koma bayan tattalin arzikin kasar da kaso 32.9 cikin 100 a rubu'i na biyu na shekara, inda nan take aka yi masa ca da ma Allah wadai.

Kudin tsarin mulkin Amurka dai ya fayyace cewa, majalisa tana iya duba lokacin zaben 'yan takara, da kuma ranar da za su kada kuri'unsu, da kuma rana ta bai daya a duk fadin Amurka.

Tun shekarar 1845 ne dai, majalisar dokokin Amurka ta tsayar da ranar Talata bayan Litinin ta farko a watan Nuwanban, wanda a wannan shekara, ta kasance 3 ga watan Nuwanba a matsayin ranar zaben shugaban kasa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China