Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NASA ta harba na'urar binciken duniyar Mars
2020-07-31 11:16:26        cri
Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka (NASA) ta bayyana cewa, na'urar binciken duniyar Mars da ta harba, ta kama hanyar ta kamar yadda aka tsara, kana ta koma cikin wani yanayi na tabbatar da tsaron kai, sa'o'i bayan harba ta a jiya Alhamis, saboda wani bangare na na'urar yana da sanyi fiye da yadda aka yi zato.

An harba na'urar ce da misalin karfe 8 saura mituna 10 na safe agogon Amurka,daga cibiyar harba taurarin dan-Adam ta Complex 41 dake tashar sojojin sama ta Cape Canaveral a jihar Florida, ta hanyar amfani da rokar Alliance Atlas V.

Da misalin karfe 11 da rabi na safe agogon kasar ta Amurka, cibiyar ta samu sako daga na'urar, abin da ke nuna cewa, na'urar ta shiga yanayi na tsaron kanta, saboda wani bangarenta yana da sanyi fiye da yadda aka yi zato, yayin da duniyar ta Mars a wannan shekara ta 2020 ta zama cikin inuwar duniyarmu, a cewar hukumar ta NASA.

A yayin da na'ura za ta shafe watanni 7 kafin ta isa duniyar Mars, ana sa ran nau'rar za ta yada zango a Jezera Crater dake duniyar ta Mars a ranar 18 ga watan Fabrairu shekarar 2021.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China