Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin marasa aikin yi a Amurka ya karu a mako na biyu a jere, yayin da yawan masu COVID-19 ma ya karu
2020-07-31 11:27:16        cri

Ma'aikatar kula da kwadago ta kasar Amurka, ta ce adadin marasa aiki a kasar ya karu zuwa miliyan 1.43 a makon da ya gabata, wanda ya karu akan na makonni biyu da suka gabata, yayin da a daya bangaren, ake fama da karuwar masu COVID-19.

A cewar ma'aikatar, zuwa ranar 25 ga wata, adadin Amurkawa dake neman tallafin da ake ba marasa aiki, ya karu da 12,000 daga 1,422,000 a makonni biyu da suka wuce.

Da wannan sabon adadi, mutane miliyan 54.1 ne suka nemi tallafin cikin makonni 19 da suka wuce, wanda ya nuna matsalar tattalin arziki da annobar COVID-19 ta haifar.

Yayin da majalisar wakilan kasar ke tafka muhawara kan tsawaita shirin bada tallafin dala 600 ga marasa aiki, wanda ake sa ran zai kawo karshe a yau Juma'a, majalisar ta ce akwai kalubale sosai, la'akari da sama da ma'aikata miliyan 30 dake karbar inshorar rashin aikin yi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China