Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shawarwarin da Xi ya gabatar a taron AIIB ya samu amincewar masana
2020-07-29 10:15:29        cri

Masana daga sassa daban-daban na duniya, sun yaba matuka da shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, yayin taron shekara-shekara na bankin zuba jarin samar da ababan more rayuwa na Asiya ko AIIB a takaice karo na 5, suna masu imanin cewa, bankin zai bunkasa ci gaba na bai daya, baya ga zama wani sabon dandalin raya alakar bangarori daban-daban.

A jawabinsa yayin taron bankin da ya gudana ranar Talata, CaVince Adhere, wani dan kasar Kenya mai bincike kan alakar Sin da Afirka, ya ce, bankin ya shirya taron ne, a daidai lokacin da duniya ke fama da annobar COVID-19 da ta kassara ci gaban tattalin arzikin duniya. Yana mai cewa, bankin ya tabbatar da kansa a matsayin wani dandalin hukumomin kudi da zai farfado da tattalin arziki da jin dadin jama'ar kasashe mambobinsa, ta hanyar samar musu da wata dama.

Ya kara da cewa, ya kamata bankin ya fito da wasu matakai na ba da tallafin kudade, da zai kai ga samar da ababan more rayuwa masu dorewa a yankuna kamar Afirka.

A nasa jawabin, Constantinos Bt Costantinos, farfesa a fannin tsara manufofin gwamnati a jami'ar Addis Ababan kasar Habasha, ya ce manyan hukumomi kamar bankin AIIB na da muhimmaci, musamman ga kasashe masu tasowa, ta yadda za su ci gajiyar bankin wajen kara bunkasa ababan more rayuwarsu, da masana'antu da bangaren aikin gona har ma su samu ci gaba kamar sauran kasashen duniya.

Da ya juya ga kasashen Afirka kuwa, masanin ya ce, shigar kasashen na Afirka a dama da su a harkokin bankin, zai ba su damar rage gibin ci gaban dake tsakaninsu da sauran kasashe. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China