Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: zaman lafiya da ci gaba ne taken wannan zamani
2020-07-28 20:49:34        cri
A Talatar nan ne aka bude taron shekara-shekara ta kafar bidiyo, na majalisar bankin AIIB karo na 5. A cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ya ce zaman lafiya da ci gaba ne taken wannan zamani da muke ciki. Shugaban ya kara da cewa, hade yankuna da ababen more rayuwa, muhimmin ginshiki ne na bunkasa ci gaban dukkanin kasashen duniya.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kamata ya yi bankin AIIB ya dora muhimmanci ga ba da hidimar samar da ci gaban daukacin mambobin sa, ya samar da jarin ababen more rayuwa mai nagarta, mai sauki kuma mai dorewa.

Kaza lika, bankin ya samar da tallafi ga ababen more rayuwa na gargajiya da na zamani, ta yadda hakan zai bude wata sabuwar hanyar raya tattalin arziki, da ci gaban zamantakewa a nahiyar Asiya, da ma sauran sassan duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China