Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi zai halarci bikin aikin kammala tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3
2020-07-30 09:30:09        cri

Gobe Jumma'a ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban rundunar sojojin kasar, zai halarci bikin aikin kammala da kaddamar da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3, bikin da zai gudana a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Tuni dai tauraron dan-Adan na 55 wanda shi ne na karshe a wannan tsari, ya fara aikin sadarwa, bayan kammala gwajin kewaya falaki da aiko da sakonni, kamar yadda ofishin kula da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na kasar Sin ya sanar a jiya Laraba.

Shi dai wannan tsarin tauraron dan-Adam na BeiDou, yana daya daga cikin tsare-tsaren shawagin taurarin dan-Adam guda hudu dake aiki a duniya, da suka hada da GPS na Amurka, da GLONASS na kasar Rasha, sai kuma Galileo na kungiyar tarayyar Turai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China