Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: ba wani mahaluki a duk inda yake da zai iya dakushe ci gaban farfadowar da kasar Sin ke yi
2020-07-30 20:56:09        cri
Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya shugabanci zaman kwararru na musayar ra'ayi a ranar Talata, inda yayin da yake tsokaci ga mahalarta taron, ya ce Sin na da niyya da kuma karfin halin tunkarar dukkanin kalubalen da ke gabanta. Don haka a cewar shugaban, ba wani mahaluki a duk inda yake a duniyar nan, ko wata kasa da za su iya dakushe ci gaban farfadowar da kasar Sin ke yi.

Xi Jinping, ya kuma jaddada muhimmancin fahimtar hakikanin yanayin tattalin arziki da ake ciki, tare da kara zurfafa sauye sauye cikin himma da kwazo.

An dai gudanar da zaman ne domin tattara ra'ayoyi, da shawarwari, game da yanayin tattalin arziki da ake ciki a kasar, da kuma aikin da ake yi a watanni 6 na biyu na shekara nan ta 2020, daga masu ruwa da tsaki da ba sa cikin JKS. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China