Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping na jagorantar aikin raya rundunar sojan kasar Sin
2020-07-30 20:42:04        cri

Idan mun dubi tarihin kasar Sin, a ranar 1 ga watan Agustar shekara ta 1927 ne aka ji karar bindigogi a birnin Nanchang na lardin Jiangxi dake kudu maso gabashin kasar, matakin da ya kasance tubalin kafa sabuwar rundunar sojan jama'ar kasar ta Sin.

Daga lokacin zuwa yanzu, wato an cika shekaru 93, rundunar sojan kasar Sin, tana bin umarnin jam'iyyar kwaminis, har ma sojojin kasar sun yi gwagwarmayar gudanar da yake-yake, wadanda suka samu dimbin nasarori daya bayan daya.

A sabon zamanin da muke ciki kuma, babban burin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ke kokarin cimmawa shi ne, raya wata rundunar sojan jama'ar kasar, wadda ke karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis, da iya samun galaba kan yake-yake, don ta zama fitacciyar rundunar soja a duk fadin duniya baki daya.

Tun bullar cutar mashako ta COVID-19, daukacin rundunonin sojan kasar Sin sun bi umarnin shugaba Xi Jinping, don sauke babban nauyin dake wuyansu. Tun ranar 24 ga watan Janairun bana, rundunar sojan kasar Sin ta tura ma'aikatan jinyarta sama da dubu hudu, cikin rukunoni uku zuwa birnin Wuhan na lardin Hubei, wadanda suka bayar da gudummawa babba ga ayyukan ganin bayan annobar.

Har wa yau, tun watan Yulin bana, ruwan saman da aka sheka kamar da bakin kwarya, ya janyo bala'in ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a sassa da dama dake kudancin kasar Sin, inda ba tare da wani jinkiri ba, sojojin kasar Sin suka taru, aka kuma tura su domin tallafawa wuraren da bala'in ya ritsa da su.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake nanata cewa, ya kamata a horas da sojojin kasar bisa bukatun yake-yake. Kuma a watan Disambar shekara ta 2012, wato bada jimawa ba da rufe babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, Xi ya ziyarci wata rundunar sojan kasar, inda ya jaddada cewa, babban tushen inganta karfin sojoji shi ne, tsaurara matakan gudanar da harkokin sojojin bisa doka.

A karkashin tsayayyen jagorancin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wadda Xi Jinping ya zama jigonta, da tunanin Xi a fannin inganta karfin rundunar soja, muddin aka nace ga bin hanyar raya rundunar soja bisa salon musamman na kasar Sin, ko shakka babu za'a iya cimma burin raya rundunar sojan kasar daga dukkan fannoni, har ta zama fitacciyar rundunar a duk fadin duniya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China