Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kaso 80 na jama'ar Amurka da aka ji ra'ayoyinsu na ganin kasarsu ta kauce hanya
2020-07-28 16:20:37        cri
A ranar 26 ga wannan wata, wato ya rage kwanaki 100 kafin zaben shugaban kasar Amurka, kamfanin CNN, da gidan rediyon CBS, da kamfanin NBC da sauran kafofin yada labaru na kasar sun gabatar da sakamakon binciken ra'ayoyin jama'a, inda aka bayyana cewa, yawan masu goyon bayan Donald Trump a jihar Florida, da ta Arizona, da ta Michigan da sauran jihohin da Trump ya cimma samun yawancin kuri'un goyon baya a shekarar 2016, ya yi kasa da yawan masu goyon bayan dan takarar jam'iyyar adawa wato Joseph Biden. Bisa binciken ra'ayoyin jama'a da kamfanin dillancin labaru na AP ya yi, kashi 80 cikin dari na jama'ar kasar da aka ji ra'ayoyinsu na ganin kasarsu ta kauce hanya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China