2020-07-29 13:14:24 cri |
Kwanan baya, Amurka ta nemi kasar Sin da ta rufe karamin ofishin jakadancinta dake birnin Houston ba tare da wani dalili ba, abun da ya jefa dangantakar kasashen biyu cikin mawuyacin hali. Wannan lamari ya jawo hankalin kafofin yada labarai na kasar Amurka sosai, inda suka yi hasashe kan makomar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labarai ta AP ta Amurka ya ba da labari a ran 27 ga wata cewa, a matsayinsu na kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya, kasashen biyu na da muradu iri daya da ba za su rabu da juna ba, kara tsananta dangantakar kasashen biyu zai kawo cikas ga kasashen biyu da ma duniya baki daya.
Alkaluman kididdigar da kwamitin kula da cinikin Amurka da Sin na Amurka ya fitar sun nuna cewa, a shekarar 2018, sha'anin fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin ya samar da guraben aikin yi kimamin miliyan 1 a Amurka. Kuma Sin kasancewar kasuwa mafi girma ga jihar Iowa da sauran jihohi a fannin amfanin gona. Wadannan jihohi na fuskantar babbar asara saboda gogayyar kasashen biyu ta fuskar ciniki.
AP ya ce, kasashen biyu na da dangantaka mai zurfi a fannin sadarwa da kwamfuta da kuma ayyukan jiyya da sauran masana'antun samar da kayayyaki da kuma kasuwanninsu. Amma, gwamnatin Amurka mai ci ta takaitawa kamfanin Huawei damar amfana da kayan gyara da fasahar irin wadannan kayayyaki na Amurka, matakin da zai lahanta hadin kai a wadannan fannoni, ban da wannan kuma, kamfanoni da dama ciki hadda kamfanonin dake Silicon Valley, za su yi asarar biliyoyin Dala.
Ban da wannan kuma, kafar watsa labarai Birtaniya BBC ta ba da bayani cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta yi tsami ba ma kawai ana kusantar babban zaben kasar Amurka ba. A farkon shekarar 2016, Donald Trump ya yi amfani da kishin Amurka, a matsayin yakin neman zabe, inda yake neman kin jinin kasar Sin. A wannan shekara, farin jinin Trump ya ragu matuka, saboda gazawar matakan gwamnati na yakar COVID-19. Har yanzu dai, Trump yana ci gaba da zargin kasar Sin don neman dora mata laifi. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China