Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnan jihar Borno ya tsallake wani hari da ake zargin na 'yan kungiyar Boko haram ne
2020-07-31 10:08:40        cri

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya tsallake wani harin kwantar bauna da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kai wa a garin Baga, dake kan iyakar tafkin Chadi, wanda ke da nisan kilomita 196 daga birnin Maiduguri na jihar dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, nan take jami'an tsaron dake tare da Gwamnan suka mayar da martani.

Majiyar ta ce lamarin ya auku ne lokacin da gwamnan ke kan hanyarsa ta zuwa sansanin 'yan gudun hijira dake yankin arewacin kasar, karkashin wani shiri na rarraba abinci.

A cewar wata kafar yada labarai ta kasar, a wani lokaci can baya, garin Baga ya kasance tungar kungiyar, har zuwa lokacin da sojoji suka sanar da kwace iko da shi a watan Fabrerun 2015, sai dai ana zargin har yanzu akwai mayakan kungiyar dake kaddamar da hare-hare.

Kawo yanzu, rundunar 'yan sanda da ta sojin kasar ba su tabbatar da aukuwar lamarin ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China