Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta yi gargadin samun ambaliyar ruwa a yankuna 102
2020-07-11 16:25:50        cri
Gwamnatin Nijeriya ta yi gargadi game da yuwuwar samun ambaliyar ruwa a yankunan kananan hukumomi 102 dake fadin jihohi 28, a lokacin daminar bana.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta kasar Muhammadu A Muhammad, wanda ya bukaci hukumomin agaji na jihohi da gwamnatocin kananan hukumomin da batun ya shafa, su zauna cikin shiri, ya kuma shawarci a wayar da kan al'ummomin yankunan kan su shirya domin a kwashe su.

Har ila yau, ya bada shawarar kwashe bola da ciyayi da sauran tsirrai daga magudanan ruwa da sauran hanyoyin ruwa, domin ba ruwan damar gudana ba tare da wani cikas ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China