Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar Soja mace ta farko mai tuka jirgin helkwafta a Nijeriya
2020-07-15 11:08:17        cri

Hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar wata soja mace ta farko mai tukin jirgin helkwafta a Nijeriya, Tolulope Arotile, sakamakon raunin da ta ji a ka.

Rundunar sojin saman Nijeriya, wadda ta tabbatar da hatsarin cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce lamarin ya auku ne a jihar Kaduna, dake arewa maso yammacin kasar.

Ta kara da cewa, Tolulope Arotile, wadda ke cikin shekaru 20, ta bada gudunmuwa a kokarin murkushe ayyukan 'yan bindiga a arewa maso tsakiyar kasar ta hanyar gudanar da ayyukan da dama.

Rundunar sojin wadda ta yi takaicin mutuwar, ta ce aikin marigayiyar ga Nijeriya na lokaci ne kalilan, amma kuma mai tasiri.

A matsayinta na mace ta farko mai tukin jirgin helkwafta a Nijeriya, Arotile ta yi fice a kasar bayan da rundunar ta yabawa sha'awar da ta nuna na aikin da ake ganin na maza ne. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China