Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a dawo zirga zirgar jiragen kasa a Najeriya bayan shafe watanni suna rufe
2020-07-26 15:49:39        cri
Ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi, yace za'a dawo da zirga zirgar jiragen kasa a Najeriyar bayan shafe watanni suna kulle sakamakon barkewar annobar COVID-19.

Layin jirgin kasa na Abuja-Kaduna, an rufe shi tun a watan Maris domin takaita bazuwar cutar, ana sa ran za'a sake bude shi a ranar Laraba mai zuwa, in ji ministan.

Sai dai Amaechi ya kara da cewa, an dauki kwararan matakan kariya domin tabbatar da kare lafiyar fasinjojin da za su yi ta'ammali da jiragen kasa a Najeriyar.

Ministan sufurin ya sanar da wannan mataki ne a lokacin da ya jaoranci gwajin sabbin taragan jiragen kasan wanda kamfanin ayyukan jiragen kasa na kasar Sin ya tura kwanan nan zuwa layukan jiragen kasan Najeriyar, kamfanin wanda ke gudanar da mafi yawan ayyukan shinfida layin dogo a kasar, wanda ya hada har da aikin zamanantar da wasu ayyukan jirgin kasa a Najeriyar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China