Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnonin Najeriya sun goyi bayan 'yar takarar shugabancin WTO
2020-07-16 14:01:50        cri
A ranar Laraba gwamnonin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga 'yar takarar Ngozi Okonjo-Iweala, na neman mukamin shugabancin kungiyar cinikayya ta duniya WTO.

Okonjo-Iweala, wacce ta taba zama ministar kudi a Najeriya kana ta taba rike ministar harkokin kasashen waje ta kasar na gajeren lokaci.

A wata sanarwa, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abubakar Bagudu, ya bukaci shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, da ya nemi goyon bayan sauran shugabannin Afrika domin samun nasarar Okonjo-Iweala domin moriyar kasar.

A cewar Bagudu, kasancewar Okonjo-Iweala a matsayin shugabar WTO zai yi matukar amfanawa cigaban nahiyar Afrika, ya kara da cewa, kungiyar gwamnonin ta yi amanna cewa za'a samu hadin kan bangarorin duniya idan aka baiwa Okonjo-Iweala shugabancin kungiyar WTO.

Roberto Azevedo, shugaban kungiyar WTO na yanzu, ya sanar da aniyarsa ta sauka daga shugabancin kungiyar a hukumance a ranar 31 ga watan Augasta, shekara guda gabanin cikar wa'adin aikinsa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China