Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harin sojojin saman Najeriya ya kashe 'yan bindiga a arewa maso yammacin kasar
2020-07-23 10:19:30        cri
Hare haren da sojojin saman Najeriya suka kaddamar ya lalata maboyar 'yan bindiga a cikin dajin Kagara dake jahar Zamfara a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, kakakin rundunar sojojin kasar ne ya bayyana hakan.

An kaddamar da harin ne a ranar Litinin bayan samun rahoton bayanan sirri dake nuna cewa akwai mayakan 'yan bindigar masu yawan gaske a dajin, a wani yanki na dajin, John Enenche, kakakin rundunar sojojin kasar ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Ya ce bayan da aka tabbatar da sahihancin bayanan sirrin ta hanyar gudanar da sintiri ta sama, an kaddamar da lugudan wuta ta jiragen sama a maboyar maharan.

A cewar kakakin, rundunar sojojin mai kula da wannan shiyya ta tura zaratan sojojin sama zuwa yankin, tare da makamai inda suka yi nasarar kashe wasu daga cikin 'yan bindigar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China