Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu cutar COVID-19 a Amurka ya karu da kusan 55,000 cikin kwana 1
2020-07-03 13:13:38        cri

Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar ya karu da 55,000 jiya, wanda ya zama sabon adadi mafi yawa da aka samu a rana guda.

Alkaluman cibiyar sun nuna cewa, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya zarce miliyan 2.7, inda ya kai 2,735,554, yayin da na wadanda suka mutu ya kai 128,684.

A cewar hukumar lafiya ta jihar Florida dake kudancin kasar, adadin sabbin mutanen da suka kamu da cutar jiya a jihar, ya sha gaban na ranar Laraba, inda ya kai 10,109.

Babban jami'in kasar mai yaki da cututtuka masu yaduwa, Anthony Fauci, ya bayyanawa majalisar dattawan kasar a ranar Talata cewa, idan har ba a dakile ci gaba da bazuwar cutar ba, adadin masu kamuwa da ita a kowacce rana ka iya kai wa 100,000. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China