Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada bukatar kara farfado da yankin arewa maso gabashin kasar
2020-07-24 19:15:47        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kara jaddada bukatar nacewa ga sabon ruhin tunani da kara aiwatar da dabarun farfado da yankin arewa maso gabashin kasar.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban rundunar sojojin kasar, ya bayyana haka ne yayin rangadin da ya gudanar a lardin Jilin dake yankin arewa maso gabashin kasar ta Sin, daga ranar Laraba zuwa Jumma'ar nan.

Yayin rangadin, shugaba Xi ya bukaci da a kara zage damtse wajen ganin an yi nasarar gina al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni gami da kawar da talauci

Xi ya kuma bayyana muhimmancin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, wanda zai fara daga shekara mai zuwa, a matsayin shirin shekaru biyar-biyar na farko, tun bayan da kasar ta kama turbar gina kanta zuwa kasa ta zamani mai sigar gurguzu.


Xi ya yi kira da a mayar da hankali wajen tsara manufofin raya kasa da ake fatan cimmawa, da shawarwari da matakai, game da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China