Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya je rangadi birnin Changchun na arewa maso gabashin kasar Sin
2020-07-24 09:56:28        cri

 

Shugaban kasar Sin kuma sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, ya je rangadi jiya, a Changchun, babban birnin lardin Jilin, dake arewa maso gabashin kasar Sin.

Xi Jinping, ya ziyarci unguwanni da makarantar horar da jami'an kula da al'umma da cibiyar nune-nunen ayyukan tsara birane da kuma hedkwatar cibiyar binciken kimiyya ta kamfanin kera motoci na FAW.

Shugaban ya samu karin haske dangane da jagorancin al'umma a matakin farko da yadda ake tsarawa da raya birane da kuma yadda ake sauye-sauye da raya kamfanoni mallakar gwamnati. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China