Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga babban taron wakilan kungiyar kishin kasa ta Sinawa yara
2020-07-24 14:13:22        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga babban taro karo na 8 na wakilan kungiyar kishin kasa ta Sinawa yara, wanda aka bude jiya Alhamis a nan birnin Beijing.

Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya jaddada muhimmancin horar da yara masu basira ta yadda za su daukaka tare da raya tsarin gurguzu mai hallayar musammam ta kasar Sin da kuma cimma burin kara bunkasa kasar.

An gudanar da taron ne ta kafofin bidiyo da wayar tarho. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China