Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya ziyarci jami'ar sufurin jiragen sama ta PLA gabanin ranar sojojin kasar
2020-07-23 20:37:48        cri
Alhamis din nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci jami'ar sufurin jiragen sama ta rundunar sojojin saman kasar a lardin Jilin dake yankin arewa maso gabashin kasar Sin.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kwamitin kolin sojojin kasar (CMC), ya kara jaddada yin gyare-gyare da kirkire-kirkire, tare da kara zage damtse don inganta harkokin koyarwa.

A madadin kwamitin koli na JKS da kwamitin kolin sojojin kasar, Xi ya mika gaisuwar ranar sojojin kasar ga daukacin sojojin 'yantar da al'umma ta PLS da 'yan sandan kwantar da tarzoma da na tsaron jama'a da dakarun kota-kwana. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China