Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya damu da batun samar wa daliban da suka kammala karatu aikin yi
2020-07-24 14:16:47        cri

Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya ziyarci kamfanin hada motoci na FAW Group dake birnin Changchun a yammacin ranar Alhamis a lokacin rangadin ziyarar aiki da yake gudanarwa a lardin Jilin na kasar.

Bayan da ya lura cewa wasu daga cikin ma'aikatan da ya hadu da su a kamfanin na FAW sabbin daliban da suka kammala karatu ne, shugaba Xi ya tattauna da su game da yanayin aikin nasu da kuma kudin shigarsu.

Xi ya lura cewa, sakamakon bullar annobar COVID-19, nau'ikan mutane kamar daliban da suka kammala karatu da ma'aikata 'yan ci rani, suna fuskantar wahalhalu wajen samun aikin yi a wannan shekarar, amma shugaban ya ce JKS da gwamnatin kasar Sin suna yin dukkan abin da ya dace wajen samar musu karin guraben ayyuka.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China