Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Ya kamata a yi kokarin raya shaanin harhada mota mai amfani da fasahar kasar Sin
2020-07-24 14:50:26        cri







A yammacin jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci cibiyar nazarin fasaha ta kamfanin harhada motoci na FAW na kasar Sin dake birnin Changchun, don ganin yadda ake gudanar da aikin kirkire-kikire, tare kuma da duba sabbin motocin da kamfanin ya kera cikin 'yanci wato tambarin "Hongqi" da dai sauransu. Xi Jinping ya ce, ya yi farin ciki matuka saboda ganin ci gaban da aka samu a wannan fanni. Kuma ya kara kwarin gwiwar kamfanonin wajen rike fasaha mai tushe don kera motoci cikin 'yanci.



An ce, an kafa wannan kamfani ne a shekarar 1953, a shekarar 1956 kuma aka samar da mota ta farko a nan kasar Sin, shugaba Mao Zedong wanda ya kafa jamhuriyyar jama'ar kasar Sin ya rada kuma ya rubuta sunan wannan mota "Jiefang" wato 'yantar da jama'a ke nan, hakan ya kawo karshen rashin samun mota kirar kasar Sin cikin 'yancin kai. A shekarar 1958, aka kera mota mai tambarin "Dongfeng" da na "Hongqi", abun da ya bude sabon shafin sha'anin kera mota na kasar Sin.


Bayan shekaru sama da 60 da suka gabata, kamfanin FAW ya samar da motoci fiye da miliyan 45.48 dake kunshe da samfuri iri daban-daban, yawan motocin da ya sayar yana sahun gaba a kasar Sin. Ban da wannan kuma, kamfanin ya kafa sansanoninsa 16 masu harhada motoci a kasashe 14 ciki hadda Afrka ta kudu da Pakistan da Mexico da Rasha da dai sauransu, kuma yana ciniki da kasashe 78. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China