Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fauci: Rashin daukar matakai ya haddasa karuwar COVID-19 a Amurka
2020-07-14 10:36:51        cri
Babban masanin cututtuka masu yaduwa na kasar Amurka kana darektan cibiyar cututtuka masu yaduwa Anthony Fauci, ya bayyana a jiya Litinin cewa, rashin rufe ko'ina a kasar, shi ya sa ake kara samun sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19.

Fauci wanda ya bayyana haka yayin zantawa ta kafar bidiyo da makarantar aikin likita ta Stanford, ya ce, kwan gaba kwan baya game da daukar matakan dakile cutar, shi yake sa cutar ke kara yaduwa a kasar.

Muddin Amurkawa ba za su yi karatun tanutsu game da wannan annoba ba, hakika wanki hula zai kai su dare. Ya ce, ya kamata a rufe ko'ina, amma a bude wurare sannu a hankali. A cewarsa Amurka ba ta ga komai ba ma, game da wannan annoba, domin har yanzu da masana kimiya na ci gaba da nazari a kokarin fito da tartibin magani da alluran riga kafin kwayar cutar. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China