Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 21 sun samu raunuka a tashin gobara a jirgin ruwan Amurka a San Diego
2020-07-13 10:22:16        cri
Kimanin mutane 21, ciki har da matuka jirgin ruwa 17 da fararen hula 4, sun samu raunuka da safiyar ranar Lahadi a sanadiyyar tashin gobara a jirgin ruwan Amurka dake sansanin sojojin ruwan kasar Amurka dake San Diego a jihar California.

A sanarwar da sojojin ruwan Amurka ta Pacific Fleet ta fitar ta ce, raunukan ba su da tsanani sosai kuma ana kula da wadanda suka ji raunin a wani asibiti bayan tashin gobarar jirgin ruwan na USS Bonhomme Richard.

Kimanin fasinjoji 160 ne ke cikin jirgin ruwan a lokacin da aka samu tashin gobarar da misalin karfe 8:30 na safe agogon wurin.

Hukumar kula da sojojin ruwan Amurka ta ce, jirgin ruwan na USS Bonhomme Richard ana yi masa kwaskwarima, jirgin yana da girma daukar mutane 1,000.

Har yanzu ba'a bayyana takamamman dalilin da ya haifar da tashin gobarar ba. Sai dai an jiyo wasu mutanen dake wajen suna bayyana cewa sun ji karar fashewar wani abu. Sashen aikin kashe gobara na birnin San Diego ya wallafa a shafin twita da safiyar wannan rana cewa, an samu fashewar wani abu a jirgin ruwan na USS Bonhomme Richard. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China