Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bill Gates ya bukaci a samar da riga kafin COVID-19 ga mutanen da suke matukar bukata
2020-07-13 14:02:18        cri

Hamshakin attajirin nan dan kasar Amurka, Bill Gates, ya yi kira da a samar da alluran riga kafin cutar COVID-19 ga kasashe da mutanen dake matukar bukata, maimakon wadanda suka sayi maganin da tsada. Yana mai cewa, dogaro ga abin da kasuwa za ta haifar, ka iya tsawaita annobar.

Mutumin da ya kirkiro manhajar Micosoft ya bayyana haka ne ta kafar bidiyo yayin taron da hukumar yaki da AIDS ta kasa da kasa ta shirya, yana mai cewa, idan muka bari magani ko riga kafi ya fada hannu masu neman riba, maimakon mutane da wuraren da suke matukar bukata, hakika ba mu san lokacin da za mu rabu da wannan annoba ba.

Hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai da hukumar lafiya ta duniya WHO, sun yi gargadin kan takarar da ba ta dace ba a kokarin da ake na samar da maganin wannan annoba, da ake ganin za ta kare rayuka da daidaita matsalar tattalin arziki da annobar ta haifar, yayin da wasu jami'ai a Washington suke nuna alamun a ba da fifiko ga Amurka. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China