![]() |
|
2020-07-21 20:40:58 cri |
Kwanan baya, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Amurka ta shigar da kamfanonin kasar Sin guda 11 cikin takardar jerin sunayen kamfanonin da za ta sanyawa takunkumi bisa hujjar "keta hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta kasar Sin".
Dangane da lamarin, Wang Wenbin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Talata a nan Beijing cewa, Amurka ta takaita kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasar Sin, kana ta shigar da kamfanonin kasar Sin masu ruwa da tsaki cikin takardar jerin sunayen kamfanonin da za ta sanyawa takunkumi bisa hujjar hakkin dan Adam. Abin da Amurka ta yi ya saba wa muhimman ka'idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa, kana tsoma baki ne a harkokin cikin gida na kasar Sin, ta kuma kawo illa ga muradun kasar Sin. A don haka, kasar Sin tana adawa da hakan. Za kuma ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka wajaba don kiyaye muradun kamfanoninta. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China