![]() |
|
2020-07-09 20:30:47 cri |
Zhao ya kara bayyana cewa, idan ana maganar cancanta, a 'yan shekarun da suka gabata, kasar Amurka ta yi amfani da fifikon Amurka a dandalin kasa da kasa, don yin watsi da alkawarin da ta yi da nauyin dake bisa wuyanta, ta yi janyewa daga yarjeniyoyi da hukumomi daban daban, yanzu ta kasance wanda ta fi kowace tada fitina a duniya. Idan ana maganar gaskiya, Zhao ya bayyana cewa, yana son ya tambayi Mike Pompeo ko gwamnatin kasarsa na iya fadar gaskiya kan sansanin nazarin kwayoyin hallitu na Fort Detrick, da "cutar taba ta lantarki", da kuma dakunan gwaje-gwajen kwayoyin hallitu da kasar ta kafa a sassa daban-daban na duniya, ko za ta iya yiwa jama'arta da sauran kasashen duniya wani bayani game da wadannan? Kan batun nauyi kuma, a cikin kasa da rabin shekara, wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar sun wuce miliyan 3, wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar sun wuce dubu 130. Lallai ya kamata gwamnatin kasar Amurka ta dauki alhakin wadannan. (Bilkisu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China