Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin Amurka na gayyatar Sin shiga shawarwarin kayyade makamai ne domin burinta na siyasa
2020-07-10 19:41:57        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, kasarsa tana nan akan matsayinta na adawa da batun kayyade makamai a tsakanin bangarori uku. Wai maganar da ake cewa, kasar Amurka na shirin gayyatar kasar Sin ne don shiga shawarwarin kayyade makamai domin cimma burinta na siyasa.

Kakakin wanda ya bayyana haka a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Juma'a, ya kara da cewa, kasar Sin tana nan akan matsayinta na adawa da shawarwari kan batun kayyade makamai a tsakanin bangarori uku, kuma kasar Amurka ta san da haka sosai. Amma duk da haka, tana ta furta wannan maganar har ma ta jirkita matsayin kasar Sin kan batun. Wannan ya nuna cewa, maganar Amurka game da shawarwarin a tsakanin bangarori uku ba da gaske take ba ko babu tabbaci a cikinsa, ta yi haka ne domin cimma burinta na siyasa.

Mun bukaci Amurka da ta hanzarta ba da amsa mai yakini kan kiran kasar Rasha game da tsawaita lokacin sabuwar yarjejeniyar rage manyan makamai, kuma bisa wannan shawara ce ta kara rage manyan makamanta, ta yadda za a samar da yanayi mai kyau ga sauran kasashe da suka mallaki makaman nukiliya don su shiga shawarwarin kwance damarar makaman nukiliya. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China