Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron baje kolin abinci na nahiyar Afrika domin karfafa tsarin samar da abinci yayin da ake fama da COVID-19
2020-07-21 13:21:51        cri
An bude taron baje kolin abinci na nahiyar Afrika a jiya Litinin, domin karfafa tsarin samar da abinci yayin da ake fama da annobar COVID-19 a duniya.

Wata sanarwa da mashirya taron suka fitar, ta ce baje kolin zai gudana ne ta dandalin intanet na "makon cinikayya na duniya" saboda matakan hana tafiye-tafiye da gwamnatoci suka sanya da nufin dakile annobar.

Taron na yini 5, zai karbi bakuncin wasu fasahohin zamani a bangaren samar da abinci da aikin gona tare da gabatar da sabbin kayayyaki da fasahohin da za su taimaka wajen bunkasa kasuwanci cikin shekaru 10 masu zuwa.

A cewar sanarwa, taron ya samu masu baje kayayyaki daga kimanin kasashe da yankuna 14, ciki har da kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China