2020-01-17 10:06:36 cri |
An yi kiyasin mutane miliyan 45 daga cikin mutane miliyan 345 a yankin hamada musamman mata da kananan yara suna fama da matsalar karancin abinci sakamakon mummunan fari, gami da ibtila'in ambaliyar ruwa, da tabarbarewar tattalin arziki dake addamar shiyyar, daraktan shirin WFP a kudancin Afrika Lola Castro shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.
Casro ya ce akwai bukatar kasa da kasa su kara kaimi don samar da tallafin gaggawa ga miliyoyin jama'a a shiyyar kudancin Afrika, da kuma zuba jarin dogon lokaci wanda zai taimakawa mutane marasa galihu a shiyyar wajen jure matsanancin sauyin yanayin dake kara ta'azzara a yankin.
WFP yana shirin samar da taimako ga mutane miliyan 8.3 da matsalar ta shafa ko kuma suke cikin bukatar taimakon gaggawa saboda matsananciyar yunwa a kasashe 8 da matsalar tafi kamari da suka hada da Zimbabwe, Zambia, Mozambique, Madagascar, Namibia, Lesotho, Eswatini da Malawi. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China