Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sauyin yanayi ya haifar da gibin abinci a kasashen SADC
2019-08-12 09:29:16        cri
Darektan kula da harkokin abinci, aikin gona da albarkatun kasa a sakatariyar kungiyar raya kasashen kudancin Afirka(SADC) Domingos Gove ya bayyana cewa, galibin kasashe mambobin kungiyar SADC 16 na fama da matsalar gibin abinci, lamarin da ya yi muni a fannin samar da abinci a shiyyar baki daya.

Jami'in ya bayyana hakan ne, ga taron manema labarai a Dar es Salaam, cibiyar kasuwancin kasar Tanzaniya, gabanin taron kolin shekara-shekara na shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar karo na 39 da aka shirya gudanarwa a ranar 17 zuwa 18 ga watan Agusta. Yana mai cewa, kasashe mambobin kungiyar na fama da wannan matsala, in ban da kasashen Afirka ta kudu da Zambia wadanda suka yi tanadin abinci.

Ya ce, yankin ya fuskanci matsalar karancin ruwan sama gami da bala'o'i kamar mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama da ta aukawa kasashe Mozambque da Malawi da Madagascar da tsibirin Comoros a baya-bayan nan, inda ta yi mummunan barnar da ta wuce tunani.

Gove ya ce, yanzu haka kwamitin da kungiyar ta kafa, yana nan yana duba yanayin da kasashe mambobin kungiyar ke ciki.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China