![]() |
|
2019-08-06 10:35:38 cri |
Josefa Sacko, kwamishiniyar AU ta hukumar kula da tattalin arzikin karkara da aikin gona ta kungiyar tarayyar Afrika, ta yi wannan gargadi a lokacin taron tattaunawa game da samar da isashen abinci na Afrika wanda aka gadanar a Kigali, babban birnin kasar Rwanda.
Tace karuwar dumamar yanayin duniya, da karancin ruwan sama da ake fuskanta a sanadiyyar sauyin yanayin sun kasance a matsayin babbar barazana ga fannin aikin gona a Afrika, kasancewar mafi yawan manoman nahiyar har yanzu suna cigaba da gudanar da tsarin noman gargajiya.
Sacko tace, Afrika tana fuskantar matsananciyar barazana sakamakon matsalar sauyin yanayi fiye da sauran sassan duniya saboda yadda nahiyar ta dogara kacokan kan aikin gona a matsayin hanyar samun abinci.
A cewarta, akwai bukatar a samar da shirin hadin gwiwa tsakanin manoma, da masu tsara dabarun shugabanci, da kungiyoyin raya cigaba, da shugabannin gwamnatocin Afrika domin aiwatar da salon aikin gona wanda zai dace da sauyin yanayin da ake fuskanta.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China