Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara gwajin cutar Korona na bai daya a duk fadin birnin Urumqi
2020-07-19 17:31:27        cri

Urumqi, babban birnin jahar Xinjiang Uygur mai cin gashin kai dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin, ya fara gwajin cuta na bai daya a duk fadin birnin bayan samun rahoton yaduwar annobar ta COVID-19 a baya bayan nan, hukumomin yankin sun sanar da hakan a ranar Asabar.

Tun daga ranar Juma'a, birnin ya fara aikin gwajin a yankunan da aka samu rahoton bullar cutar, binciken ya hada da mutanen da ake zargin sun kamu, da wadanda suke dauke da cutar amma ba su nuna alamunta ba ko kuma mutanen dake fama da zazzabi. Za'a gudanar da aikin gwaje gwajen a tsakanin al'ummomin sauran yankuna, da kamfanoni, da cibiyoyin a zagaye na biyu, a cewar Zhang Wei, daraktan hukumar lafiyar Urumqi, wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai.

Zhang ya ce, an yi nasarar shawo kan annobar a birnin, sai dai matakan kandagarki da na kariyar da ake daukar ba su gamsar ba.

Daga ranar Laraba zuwa tsakar ranar Asabar, a jahar Xinjiang an samu kimanin mutane 17 da aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 da wasu mutanen 23 da ba su nuna alamun kamuwa da cutar ba, dukkansu a birnin Urumqi, inji jami'in hukumar lafiyar shiyyar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China