Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Beijing ta sanar da rahoton karin mutane 14 sun kamu da COVID-19
2020-06-28 16:13:05        cri
Hukumar lafiyar birnin Beijing ta sanar karin mutane 14 sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a cikin kwaryar birnin, sannan an samu rahoton mutane 3 sun kamu wadanda ba su nuna alamomin kamuwa da cutar ba.

A rahoton da hukumar ke fitarwa kullum ta ce, a ranar Asabar an samu karin mutum guda da ake zaton yana dauke da cutar.

Daga ranar 11 zuwa 27 ga watan Yuni, jimillar mutane 311 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a birnin Beijing wanda aka samu yaduwar cutar a cikin gida, a halin yanzu dukkannin majinyatan suna samun kulawar jami'an lafiya. Haka zalika, akwai wasu mutanen 26 da ba su nuna alamomin kamuwa da cutar ba, suke karkashin kulawar likitoci.

An sake samun bullar cutar ne a birnin Beijing bayan shafe tsawon kwanaki 57 ba tare da samun sabon rahoton kamuwa da cutar ba a cikin gida. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China