Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu yan kasuwar Xinfadi sun koma bakin aikinsu bayan killacewa
2020-07-13 11:27:23        cri

A kwanakin baya ne, aka rufe kasuwar Xinfadi, bayan da aka samu rahoton bullar COVID-19 a kasuwar dake kudancin birnin Beijing, aka kuma killace 'yan kasuwa da wasu rukunin mutane da ake ganin suna da hadarin kamuwa da wannan cuta da ta bulla a kasuwar. Ya zuwa yanzu, an kammala aikin kashe kwayoyin cutar a kasuwar, an kuma sake bude ta, amma ban da rumfar sayar da naman shanu da rago zuwa wani lokaci, saboda gano asalin yadda cutar ta barke.

Bayan killace 'yan kasuwar ta Xinfadi fiye da 1000 na tsawo kwanaki 28, yanzu sun kammala wadannan kwanaki, har wasu sun bude shagunansu dake kasuwar.

Niu Jianzhong wanda yake kulawa da kasuwar ya ce, 'yan kasuwar sun gamu da wasu matsaloli yayin da suke zama a gida, sai dai yanzu anan kokarin taimaka musu wajen warware su nan da nan. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China