Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta daura damarar cimma nasarar manufofin ci gaban tattalin arziki da jin dadin jamaa da take fatan samu a bana
2020-07-13 10:39:40        cri

Alkaluman ci gaban tattalin arziki da kasar Sin ta fitar a baya-bayan nan sun bayyana cewa, kasar tana aiki tukuru wajen ganin ta cimma nasarar manufofin ci gaban tattalin arziki da jin dadin jama'a da take fatan cimmawa a bana.

Wasu alkaluma da hukumar zirga-zirgar jiragen kasa ta kasar ta fitar sun nuna cewa, a rubu'in farko na wannan shekara, yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu ta jiragen kasa, ya kai tan biliyan 1.69, karuwar kaso 3.6 cikin 100 kan shekarar da ta gabata.

Haka kuma wasu sabbin alkaluma da hukumar kula da harkokin bankunan kasar ta fitar, sun nuna cewa, an jinkirtar kudaden ruwa na rancen da kanana da matsakaitan kamfanoni ya kamata su biya, wanda ya tassama sama da RMB Yuan triliyan 1.8. Bugu da kari, a watanni shida na farko wannan shekara, rancen da wasu hukumomin kudi suka bayar ya karu zuwa sama da Yuan Triliyan 12, matakin da ya taimakawa matakan kandagarki da hana yaduwar COVID-19 da raya tattalin arziki da jin dadin jama'a.

A hannu guda kuma, wani rahoton cibiyar jigilar kayayyaki ta ruwa ta kasa da kasa ta Xinhua-Baltic na shekarar 2020, da aka fitar a Shanghai da Singapore, ya nuna cewa, a karon farko birnin Shanghai ya kasance cikin cibiyoyin ukun farko da ke sahun gaba a fannin jigilar kayayyaki ta ruwa na kasa da kasa, Singapore na matsayi na biyu, yayin birnin London ke mataki na farko. Kididdiga na nuna cewa, a shekarar 2019, yawan kwantenonin da suka ratsa tashar ruwan Shanghai sun kai miliyan 43.3, inda ta zama ta farko a duniya shekaru goma a jere. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China