Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
PPI din na kasar Sin a watan Yuni ya karu
2020-07-09 21:33:14        cri
Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a yau Alhamis, sun nuna cewa, ma'aunin farashin kayayyakin da masana'antu ke samarwa wato PPI a takaice na kasar Sin a watan Yuni ya karu da 0.4% kan na watan Mayu, adadin da ya ragu da 3.0% bisa na makamancin lokacin bara. Mai bincike na musamman a ofishin masu ba da shawara na majalisar gudanarwar kasar Yao Jingyuan yana ganin cewa, wannan ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar na farfadowa.

Yao ya kara da cewa, sakamakon dawowa bakin aiki, tattalin arziki ya soma farfadowa, hakan ya sa bukatu ke karuwa, ta yadda farashin PPI ya sauya. Yanzu haka, masana'antu na ci gaba da komawa bakin aiki, kuma yanayin zai inganta a rubu'i na uku da na hudu na shekarar da muke ciki. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China