Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Farfadowar tattalin arzikin Sin zai samar da sabbin damammaki ga duniya
2020-07-16 20:41:45        cri

A yau Alhamis, alkaluman hukumar kididdigar kasar Sin sun nuna cewa, a cikin rubu'in farko na bana, tattalin arzikin kasar ya ragu, amma a rubu'in biyu, ya karu da kaso 3.2 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokaci a bara.

Jaridar The Wall Street Journal ta bayyana cewa, kasar Sin ita ce kasa ta farko da ta cimma burin samun karuwar tattalin arziki a duniya, tun bayan barkewar annobar COVID-19. Kaza lika kafar CNN ta Amurka, ta gabatar da sharhi dake cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya karu, wanda hakan albishir ne ga sauran sassan duniya. An kuma lura cewa, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin yana kawo haske da fata ga daukacin duniya.

Game da hakan, shugaban cibiyar nazarin tattalin arziki ta Peterson dake Amurka Adam Posen, ya yi nuni da cewa, matakan da suka dace da gwamnatin kasar Sin ta dauka na dakile annobar dalilan da suka sa ta cimma burin farfado da tattalin arzikin kasar.

Kamfanonin kasar Sin da dama su ma sun bayyana cewa, sabbin manufofin da gwamnatin kasar ta fitar, domin sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki, suna taka babbar rawa ga gudanarwar harkokin kamfanoninsu, haka kuma sun taimaka wajem samar da aikin yi ga al'ummun kasar.

Kana gwamnatin kasar Sin tana dukufa wajen aiwatar da manufar bude kofa ga ketare, don haka 'yan kasuwa da suka zo kasar domin zuba jari, suna cike da imani ga makomar kasar matuka.

Hakika kasar Sin ita ma tana fuskantar kalubaloli da dama, yayin da take kokarin raya tattalin ariki, saboda yaduwar annobar a sauran sassan duniya, amma duk da haka, tana cike da imani, ganin cewa ko shakka babu, za ta haye wahallalun dake gabanta, kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cikin wasikar sa ga dandalin manyan jami'an kamfanonin kasa da kasa na duniya a jiya Laraba, inda ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa kwaskwarima, kuma za ta ci gaba da bude kofa ga ketare. Ban da haka za ta ci gaba da aiwatar da sabbin manofofin sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin da ta fitar, domin samar da muhallin kasuwanci mai inganci ga kamfanonin kasar Sin, da na kasashen waje baki daya, tare kuma da samar da sabbin damammaki, da sabuwar makoma ga daukacin kasashen duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China