Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birnin Rongcheng na lardin Shandong na ba da kulawa sosai ga tsoffi
2020-07-14 13:20:47        cri

Birnin Rongcheng na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin ya samar da kyautar abinci iri daban-daban masu dadin ci ga tsoffin da shekarunsu ya haura 80 a duniya.

A ranar 4 ga wata, a lokaci daya ne an kaddamar da irin wadannan dakuna masu samarwa tsoffi abinci kyauta kimanin 115 a kauyuka daban-daban na birnin, inda tsoffi suke cinye nau'o'in abinci masu dimbin yawa cikin farin ciki.

Ya zuwa yanzu, an kafa irin wadannan dakunan ci abinci har 291 a yankuna daban daban na birnin, inda aka yi amfani da 137 daga cikinsu, kuma yawan tsoffin da suke cin gajiya ya kai 1766 a ko wace rana. Masu aikin sa kai ne suke gudanar da wadannan ayyuka. Kwamitin mazauna kauyuka ya kafa rukunin masu aikin sa kai dake dafa abinci, da kuma karfafawa masu aikin sa kai gwiwar shiga aikin samarwa tsoffi abinci. Wadanda suka shiga aikin za su samu makin amana, wanda maki ne da ake amfani da shi don cin gajiyar manufar gatanci a fannin biyan kudin wutar lantarki da kudin mota har ma da samun rancen kudi da sauran ayyuka fiye da 180.

Har illa yau, runkunonin masu aikin sa kai da suka yi rajista a birnin ya kai 1496, yawan mambobinsu kuma ya zarce dubu 155. Daga cikinsu, masu aikin sa kai daga kauyuka ya kai dubu 102, inda yawansu ya kai kashi 35.5% bisa na dukkanin mazauna. Wadannan mutane masu aikin sa kai sun gudanar da ayyukan iri daban-daban a kauyuka daban-daban. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China